Jirgin yakin Amurka sumfurin B-52 ya isa Koriya ta Kudu bayan gwajin makamin nukuliyar Koriya ta Arewa
Jirgin yakin Amurka sumfurin B-52 ya isa Koriya ta Kudu bisa wani matakin mayar da martani ga kasar Koriya ta Arewa game da gwajin makamin nukuliyar da ta yi baya bayan nan, in ji kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Kudu, Yonhap, da ya raiwato majiyoyin soja.
Wannan jirgin yaki mai cin dogon zango, ya tashi daga sansanin sojan Anderson da ke tsibirin Guam a yankin Pacific, sannan ya sauka a ranar Lahadi da rana a sansanin sojan Osan da ke gabashin Koriya ta Kudu. Sanarwar zuwan nasa an yi ta cikin hadin gwiwa tsakanin rundunonin saman Amurka da na Koriya ta Kudu, in ji Yonhap. (Maman Ada)