Da yake magana a yayin bude taron kwamitin kimanta matsalar tsaro a filayen jiragen sama, a ranar Jumma'a a birnin Abuja, ministan dake kula da harkokin sufurin jagaren sama Hadi Sirika ya amince cewa hadarun baya bayan nan a filayen jiargen saman Najeriya na janyo fargaba.
A cewarsa, ya kamata a baiwa tsaron filayen jiragen sama muhimmanci sosai.
Akwai karya dokoki a bangaren tsaro a cikin filayen jiragen sama, lamarin dake janyo damuwa ga kasa a cikin gida da ma waje, in ji mista Hadi Sirika.
Jami'in ya bayyana cewa kwamitin da ake dorawa nauyin kimanta batun tsaro a filayen jiragen sama zai kuma samar da kudurori ga filayen jiragen sama game da lamarin da ya shafi abin da suka rasa. (Maman Ada)