Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, Ayodele Famuyiwa, ya tabbatar a cikin wata sanarwa cewa wani jirgin sama mai tuka kansa na rundunar dake aikin kalato bayanai, sanya ido da kuma tattance wurare ya gano wani sansanin mayakan kungiyar Boko Haram a Garin Moloma, mai tazarar kilomita daya daga arewacin dajin Sambisa, kafin a kaddamar da luguden wuta.
Karar fashewa da dama da tashin wuta sun turmuke a sansanin, kamar yadda ake gani a cikin bidiyon da jirgin yakin mai sarrafa kansa ya dauka, lamarin da ake kyautata zaton cewa wani siton man fetur ne, makamai ko kuma na harsasai, in ji mista Famuyiwa.
A cewar kakakin, wannan hari ya kasance wata babbar karaya ga kungiyar Boko Haram, kuma muhimmiyar nasara ga yakin da ake da wannan kungiyar ta'addanci.
Dajin Sambisa, musammun ma yankin tsaunuka na Gwoza dake kusa da iyaka da kasar Kamaru, ya kasance wani wurin da mayakan kungiyar Boko Haram suke amfani da shi a matsayin wata mabuyarsu. (Maman Ada)