A kalla mutane 85 suka mutu a wannan hari. Maharan sun rika harbi kan mazauna wurin kafin kuma su afkawa kauyen wuta.
A cikin wata sanarwa, mambobin kwamitin sulhu sun isar da ta'aziyarsu ga iyalai da abokan wadanda lamarin ya rutsa dasu, tare da jaje ga al'umma da gwamnatin Najeriya.
Kwamitin ya nuna yabo da kokarin wannan shiyya, musammun game da kafa rundunar hadin gwiwa domin yaki da kungiyar Boko Harma yadda ya kamata, tare kuma da bada kwarin gwiwa wajen kara samun nasarori a wannan fanni. Mambobin kwamitin sun jaddada wajabcin ganin an gurfanar da masu hannu game da wadannan hare hare gaban kotu.
Birnin Maiduguri, na kunshe da yawan mutane kimanin miliyan 2.6, kuma miliyan 1.6 sun kasance 'yan gudun hijira a cewar MDD, birnin da ya sha fama da hare haren ta'addanci sau da yawa a wadannan watanni na baya baya nan.
Kungiyar Boko Haram ta bullo a birnin na Maiduguri a shekarar 2002, kafin a shekarar 2009 ta zafafa hare harenta da suka kashe mutane fiye da dubu 17 a Najeriya da kuma tilastawa wasu mutane miliyan 2.6 barin muhalinsu. (Maman Ada)