Shugaban majalisar tarayyar Turai Martin Schulz ya tarbi Muhammadu Buhari, da ya zama shugaban Najeriya a cikin watan Mayun shekarar 2015, tare da nuna yabo kan muhimman sauye sauyen da ya bullo da su musammun ma ta fuskar yaki da ta'addanci gaban yawaitar ayyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.
A cikin jawabinsa, mista Buhari ya nuna godiya ga yawan kasashen tarayyar EU da suka bada kokari wajen ganin an ceto 'yan matan garin Chibok da aka sace a cikin watan Afrilun shekarar 2014, a arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya janyo allawadai a duniya baki daya.
Ta fuskar yaki da ta'addanci, "muna iyakacin kokari" in ji shugaban Najeriya a gaban 'yan majalisun tarayyar Turai. "An karya lagon kungiyar Boko Haram sosai na kai manyan hare hare a sassan kasa" in ji shugaba Buhari. (Maman Ada)