A ta bakin kakakin hukumar ta NCAA Muhtar Usman, an sanya takunkumin ne domin bada damar gudanar da cikakken bincike, game da ko kamfanin na bin ka'idojin da suka wajaba na sufurin jiragen sama ko a'a.
Usman ya ce daukar wannan mataki bai ci karo da matakin da ake dauka na gudanar da cikakken bincike, game da musabbabin aukuwar hadarin ba, hasalima dai a cewar sa matakin da NCAAn ta dauka, zai dada taimakawa cimma nasarar binciken da ake yi.
A ranar Larabar data gabata ne dai Helikwaftan kamfanin Bristow ya auka tekun kasar a jihar Legas, ko da yake dukkanin fasinjojin dake cikin sa su 11, da matukan sa biyu sun tsira da rayukan su.(Saminu Alhassan)