Kamar yadda Ministan shari'ar kasar Abubakar Malami yayi bayani cikin wata sanarwa da ya fitar yace kudaden hukumar yaki da laifukan da suka shafi kudaden kasar wato EFCC ce ta kwato su.
Malami yace matsayin da laifuffukan da suka shafi kudade ya kai koli a muni saboda ba kawai bangaren kudi da ya samu matsala ba saboda yadda aka wargaza tsarin shi har ma da bangaren shari'a saboda rashin sahihanin tsarin da za'a bi a shari'a , raunin hukumomin tsaro da rashin kayan aiki a bangaren shari'an daga sauran bangarori daban daban.
A watan jiya, Gwamnatin Najeriyar ta ce ana shirin yin shari'a wassu manyan jami'an gwamnati a kalla su 55 da aka same su da laifin wawushe kudin kasa lokacin da suke aiki karkashin gwamnatocin da suka shude.(Fatimah Jibril)