Sin za ta tura kwararru don halartar aikin lalata makamai masu guba na kasar Syria
A wani labarin kuma, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin cewa, gwamnatin kasar Syria ta mika takarda game da dukkan makamai masu guban da ta mallaka ga kungiyar hana yin amfani da makamai masu guba ta duniya, wannan mataki ne mai yakini bayan da kasar Syria ta sanar da kokarinta na shiga yarjejeniyar hana yin amfani da makamai masu guba. Kasar Sin ta nuna maraba game da wannan batu, kana ta nuna goyon baya ga kungiyar hana yin amfani da makamai masu guba da ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa kan wannan batu, Sin tana son yin kokari tare da bangarori daban daban wajen sa kaimi ga kungiyar da ta tsaida kudurin kawar da makamai masu guba a Syria cikin hanzari.
Ban da wannan kuma, Hong Lei ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan kungiyar, da tura kwararru don halartar aikin da abin ya shafa. (Zainab)