in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga bangarori daban daban da su daidaita batun Syria karkashin kulawar MDD
2013-09-16 20:28:21 cri
A ranar Litinin 16 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing cewa, kamata ya yi a sa kaimi ga yunkurin daidaita batun Syria a siyasance tare da lalata makamai masu guba, a kokarin daidaita wannan batu a karkashin kulawar MDD tun cikin lokaci.

Kafin wannan kuma, ministocin harkokin waje na Amurka da Rasha sun daddale yarjejeniyar daidaita batun makamai masu guba na Syria a Geneva. Mr Hong wanda ya fadi haka lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

Ya ce, Sin na maraba da yarjejeniyar da Amurka da Rasha suka daddale a kan wannan batu, da fatan za a tabbatar da gudanar da hakan yadda ya kamata. Bugu da kari in ji shi, Sin na kira da a tsagaita bude wuta a Syria, a kokarin samar da yanayi mai kyau wajen fara lalata makamai masu guba da kiran taron duniya karo na biyu na Geneva tun cikin lokaci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China