in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi tir da harin da aka kaiwa ofishin jakadancin kasar waje dake kasar Syria
2013-09-23 20:34:33 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Litinin 23 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi tir da harin da aka kaiwa ofishin jakadancin wata kasa dake kasar Syria.

Hong Lei ya ce, kasar Sin ta nuna kulawa sosai ga harin da aka kaiwa ofishin jakadancin kasar Rasha dake kasar Syria a ranar Lahadi 22 ga wata, kana ta jajantawa wadanda suka raunata, Sin ta yi Allah wadai da dukkan ayyukan kai hari ga ofisoshin jakadancin kasashen waje dake kasar Syria, kuma ta kalubalanci bangarori daban daban da abin ya shafa da su bi yarjejeniyar kiyaye huldar diplomasiyya ta Vienna da tabbatar da tsaron jakadu da ma'aikatan ofisoshin jakadancin kasashen waje dake kasar Syria. Ban da wannan kuma, Hong ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Syria da su tsagaita bude wuta da yin shawarwarin siyasa cikin hanzari don maido da zaman lafiya a kasar nan da nan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China