in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da tallafawa kasar Syria ta fuskar lalata makamanta masu guba
2013-12-19 18:12:55 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying, ta bayyana a Alhamis 19 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta dade tana nuna goyon baya ga aikin lalata makamai masu guba da MDD da kungiyar kawar da makamai masu guba suke aiwatarwa a kasar Syria, kuma tana fatan ganin za a kammala aikin lami lafiya.

Wasu kafofin watsa labaru sun ba da labarin cewa, kungiyar kawar da makamai masu guba ta zartas da shirin ci gaba da gudanar da aikin lalata makamai masu guba a kasar Syria a ranar 17 ga wata, inda ta nuna yabo ga kasar Sin da ta Rasha kan yadda suka tallafawa aikin kau da makaman ta hanyar samar da jiragen ruwa da ba da kariya ga jiragen.

Dangane da wannan labarin da aka bayar, Madam Hua ta bayyana a taron manema labaru da aka kira a ranar 19 ga wata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin yin hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa don taimakawa aikin lalata makamai masu guba na kasar ta Syria. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China