Babban magatakarda na MDD Ban Ki-Moon ya sanar da cewar, za'a yi taron Geneva karo na biyu a ranar 22 ga watan Janairun shekara mai zuwa.
A game da lamarin, kasar Sin ta bakin kakanin ma'aikatar harkokin wajen kasar Qin Gang ta ce, wannan ci-gaba yana da muhimmanci wajen aiwatar da kudiri mai lamba 2118 na kwamitin tsaron MDD., sannan zai ingiza warware matsalar a siyasance, wanda shi ne abin da kasar Sin ta dade tana kiran a bi.
Haka kuma Sin ta yi kira ga dukkannin bangarorin da al'amarin Syria ya shafa da su mai da muhimmanci a kan muradun kasa da na al'ummar kasar, su shiga tattaunawar siyasa, su kuma yi aiki da sauran kasashen duniya wajen shirya babban taron.
A fadar Qin Gang, kasar Sin za ta ba da nata gudummuwa a game da wannan taro.(Fatimah)