in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa kaimin fara shawarwarin shimfida zaman lafiya a Syria bisa shirin da aka tsara
2016-01-19 11:30:15 cri
Mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq, ya bayyana a jiya Litinin cewa, a halin yanzu bangarori daban daban da rikicin Syria ya shafa, ba su kai ga cimma daidaito ba, game da kungiyoyin da za a gayyata daga bangaren 'yan adawa, domin tattauna batun siyasar kasar Syria.

Mr. Haq ya bayyana hakan ne ga taron mane ma labarai, yayin da yake karin haske game da shawarwarin shimfida zaman lafiya da ake fatan budewa a cikin mako mai zuwa, matakin da ya ce MDD za ta sa kaimi ga tabbatar nasarar sa.

Ya ce rukunin kasa da kasa mai tallafawa sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a kasar Syria, na kokarin cimma daidaito kan kungiyoyin 'yan adawa na kasar Syria da za a gayyata domin shiga shawarwarin, kafin MDD ta fidda sakon gayyata ga bangarorin.

Tuni dai babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi kira ga bangarori daban daban da su cimma daidaito kan wannan batu. Kuma burin MDDr a halin yanzu shi ne sa kaimi ga gudanar da shawarwarin bisa tsarin da aka fidda, wato na gudanar zaman a ranar 25 ga wata a birnin Geneva.

Kaza lika kwamitin sulhun MDD ya gudanar da shawarwari a wannan rana, inda yayin tattaunawar aka saurari bayanin da manzon babban magatakardar MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura ya gabatar, game da yanayin shirya zaman shawarwarin na kasar Syria. Shugaban kwamitin sulhun a wannan karo, kuma zaunannen wakilin kasar Uruguay ya bayyana wa kafofin watsa labaru bayan shawarwarin cewa, kwamitin yana kokarin sa kaimi ga fara shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar Syria bisa shirin da aka tsara. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China