Jami'an biyu sun cimma wannan matsaya ne a yayin tattaunawa ta wayar tarho.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewar da shugabannin kasashen Amurka da Rasha suka yi ne na lalubo hanyoyin diflomasiyya don warware rikicin na Syria, sannan tattaunawar tasu za ta hada har da batun rikicin Ukraine.
Mai Magana da yawun ministan harkokin wajen Rasha Maria Zakharova, ta ce tattaunawar za ta fi mayar da hankali ne kan batun da ya shafi yankunan kasar Syria.
Ko a ranar Larabar da ta gabata ma, an gudanar da tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka da kuma MDD kan batun samar da zaman lafiya a Syria, kuma bangarorin uku sun gabatar da shawarwari dabam dabam ciki har da bukatar gudanar da taron tattaunawa don warware rikicin Syria, inda bangarorin suka gabatar da shawarar gudanar da wani taro a Geneva ta kasar Switzerlanda a ranar 25 ga watan nan da muke ciki.
Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bukaci a aiwatar da tattaunawar bisa yarjejeniyar MDD ta Vienna mai lamba 2254, wacce ta amince a shigar da dukkan bangarorin adawa na Syria cikin tattaunawar.(Ahmad Fagam)