Mataimakin Ministan hulda da kasashen waje da hadin gwiwa Luwellyn Sanders ya bayyana a lokacin kammara da shirin taron cewa fatan su ne cewa shirin samar ma matasa ayyukan yi na kungiyar AU ya biyo bayan imanin da ake da shi cewar ayyukan sa kai da matasa za su yi zai iya kawo sauyi mai ma'ana ya kumma gaggauta hanyar cigaba.
Yace kowa yana iya bada nashi lokacin da karfin shi domin samun zaman lafiya da cigaba a nahiyar baki daya. A don haka sai ya bada kwarin gwiwa ga matasan nahiyar da su yi aiki domin cigaban nahiyar.
Matasan dai za'a rarraba su aiki ne a nahiyar banda asalin kasar su inda za'a hada su da kungiyoin domin suyi ayyukan sa kai.
Luwellyn Sanders ya ce Gwamnatin kasar Afrika ta kudu tana goyon bayan ayyukan sa kai na matasa kwarai wanda kungiyar Tarayyar kasashen Afruika AU ta bullo da shi.
Shirin dai na daga cikin wadanda kungiyar ta AU ta shirya domin mai da hankali a kan samar da dogaro da kai wanda yake daga cikin manufofin kungiyar, kuma kasar Afrika ta kudu na daga cikin wadanda suka rattaba hannu akan yarjejeniyar in ji Mr. Landers.
Ya kuma yi bayanin cewa tsarin harkokin wajen kasar yana tafiya ne bisa manufofin nahiyar baki daya, na nemar ma yankuna da nahiyar cigaba da kuma yalwatuwa a cikin gida.
Daga nan sai ya ce har jam'iyya mai mulkin kasar ANC ita ma a ko da yaushe tana da wannan manufa na cigaban nahiyar.(Fatimah Jibril)