Ta'addanci da tashin hankali na masu tsattsauran ra'ayi ya rage daya daga cikin damuwar kungiyar, kuma kasashen Afrika in ji shi, dole su inganta kokarin da suke yi na dakile wannan matsala tare da magance duk wani dalilin da ke taimaka masu bazuwa.
Mr. Smail Chergui a cikin jawabin da ya yi wajen bude taron shekara shekara karo na 9 na cibiyar bincike da nazari kan ta'addanci na Afrika, ya ce kungiyar AU da cibiyar suna ci gaba da taimaka ma mambobi kasashe a nasu kokarin na ganin an hana kungiyoyin 'yan ta'adda samun sabbin dabaru da kuma kudin tafiyar da ayyukansu.
A cewar kwamishinan zaman lafiya da tsaro na kungiyar AUn, yanayin tsaro a nahiyar yana tabarbarewa, sannan ana fuskantar barazanar ta'addanci da kungiyar 'yan ta'adda dake da alaka da DAESH, yana mai bayanin cewa dakile ta'addanci ya rage babban kalubale dake fuskantar nahiyar. (Fatimah Jibril)