A cikin sanarwarsa, Ban Ki-moon ya jaddada cewa, harin ba zai rage kwarin gwiwar yin hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar AU da tawagar musamman ta AU kan batun Somaliya ba a kokarinsu na nuna goyon baya ga jama'a da gwamnatin kasar Somaliya.
A nasa bangare, kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da wannan danyen aiki da babbar murya a cikin sanarwarsa, kuma ya nuna goyon bayansa ga tawagar musamman ta AU kan batun Somaliya a kokarinta na yaki da ta'addanci da barazanar kungiyoyi masu dauke da makamai a Somaliya.
Kungiyar Al-Shabaab ta kai hari kan wani sansanin soja na kungiyar AU dake yankin Gedo na kudancin Somaliya a jiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kungiyar AU da dama.(Fatima)