Adadin na'urorin nukiliya na samar da wutar lantarki da ake ginawa a Sin yana kan gaba a duniya
A yau ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fidda takardar bayani game da matakan yin rigakafi kan hadarin makamashin nukiliya a kasar Sin, inda ya nuna cewa, ya zuwa karshen watan Oktoba na shekarar 2015, akwai na'urorin nukiliya na samar da wutar lantarki guda 27 da ke aiki a fadin kasar ta Sin, kuma karfin wutar lantarki da suke samarwa ya kai kilowatt miliyan 25.5, haka kuma, adadin na'urorin nukiliya na samar da wutar lantarki da ake ginawa a kasar ya kai 25, yayin da karfin wutar lantarki da za su samar zai kai kilowatt 27.51, lamarin da ya nuna cewa, a halin yanzu, adadin na'urorin nukiliya na samar da wutar lantarki da ake ginawa a Sin yana kan gaba cikin kasashen duniya.
Bugu da kari, bisa takardar bayanin da aka fidda, ya nuna cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen neman ci gaba yayin dake mai da hankali kan kiyaye tsaron kasa, haka kuma, tana aiwatar da manufofinta na amfani da makamashin nukiliya cikin yanayin tsaro yadda ya kamata, inda take amfani da fasahohin zamani domin raya makamashin nukiliya wajen samar da wutar lantarki. (Maryam)