Ofishin kula da harkokin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fidda takardar bayanai game da shirin ko-ta-kwana kan batun nukiliya a yau Laraba, wannan ita ce takardar bayanai ta farko da ke shafar batun nukiliya da Sin ta fitar. A cikin takardar, an ambato batun nukiliyar don shirin ko-ta-kwana, da manufar da ake bi wajen daidaita batun nukiliyar, da inganta kwarewar daidaita matsalolin nukiliya da kuma yin atisaye game da shirin ko-ta-kwana da ba da horo, da fadakar da jama'a, kana da kirkiro da sabbin dabarun yin amfani da kimiyya da fasaha don gudanar da shirin ko-ta-kwana, sai kuma inganta mu'amala da hadin gwiwa game da wannan batun.
An bayyana abubuwa da takarda ta kunsa bisa tunanin tabbatar da tsaron nukiliyar ne domin tsaron kasar. A cikin takardar, an ce, Sin ta dora muhimmanci sosai game da batun raya nukiliyar ne don zaman lafiya, da kuma kare kanta daga dukkan wata barazanar tsaro, da yin amfani da manufar tsaro don sa kaimi ga samun bunkasuwa. (Bako)