A yau Laraba ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ba da wata sanarwa da ke nuna rashin amincewa dangane da gwajin makamin nukiliya da kasar Korea ta Arewa ta yi duk da cewa, kasashen duniya ma sun nuna rashin amincewarsu da wannan mataki.
Kasar Sin na bayyana kudurinta na tsayawa tsayin daka na tabbatar da ganin an kawar da nukiliya a zirin Koriya, hana yaduwar nukiliya da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabashin Asiya.
Bugu da kari, kasar Sin ta kalubalanci Korea ta Arewa da ta cika alkawarinta na kawar da nukiliya a cikin kasar, ta kuma dakatar da duk wasu matakan da za su dagula al'amura.
Kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Korea da yankin arewa maso gabashin Asiya na dacewa da moriyar sassa daban daban. Kasar Sin za ta kara azama na ganin babu nukiliya a zirin Koriya, tare da warware batun nukiliyar zirin a yayin shawarwari tsakanin bangarori 6. (Tasallah Yuan)