Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba da takardar bayani kan gaggauta tinkarar batun tsaron nukiliya a yau Laraba cewa, kasar Sin mamba ce ta kungiyar IAEA, ta yi ta kokarin kafa tsarin tinkarar batun tsaron nukiliya tare da kasashen duniya, ta yadda, kasashen duniya za su iya yin amfani da sakamakon bunkasuwar makamashin nukiliya cikin adalci. Kasar Sin ta yi hadin gwiwa a fannoni da dama tare da kungiyar IAEA da kuma sauran kungiyoyin kasa da kasa, tare da kara yin hadin gwiwa da musayar ra'ayi tare da kasashen da batun ya shafa a fannin tinkarar batun tsaron nukiliya cikin gaggawa.(Lami)