in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi na'am kan aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran
2015-10-19 10:00:02 cri

A jiya Lahadi, kasar Sin ta bayyana goyon bayanta kan aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, sannan ta bukaci da a ci gaba da daukar makatan da suka dace domin samun nasarar shirin.

A wata sanarwa wadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta raba wa manema labarai, ta bayyana cewar, shirin aiwatar da batun nukiliyar Iran babban ci gaba ne, kuma akwai bukatar dukkanin bangarorin da lamarin ya shafa, su yi aiki tare domin tabbatar da cimma burin da aka sa a gaba.

An dai cimma matsaya kan shirin nukiliyar ne a yayin wata ganawa tsakanin Iran da kasashen duniya masu kujerun din din din a MDD 5 da kuma Jamus a birnin Vienna a ranar 20 ga watan Yuli, kuma daga ranar da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar, an bai wa Iran wa'adin watanni 3 ne da ta aiwatar da shirin.

Sanarwar ta kara da cewar, kasar Iran da manyan kasashen 6 sun goyi bayan yarjejeniyar nukilyar ta Iran, kuma sun sha alwashin ganin an aiwatar da shi kamar yadda aka amince tun a baya wato watanni 3 da suka gabata.

Hua, ta ce, kasar Sin na da kyakkyawar fatar ganin an aiwatar da shirin, lamarin da ya sa ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen tuntubar Amurka da ita kanta kasar Iran kan batun.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China