in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na Sin ya yi shawarwari da takwaransa na Afghanistan
2016-01-26 20:29:06 cri

A yau Talata 26 ga wata ne ministan harkokin waje na Sin Wang Yi, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Afghanistan, Salahuddin Rabbani a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar ta su, Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, kasancewar makwabciyar kasar Afghanistan, Sin tana nuna cikakken goyon baya ga samar da sulhu a kasar ta Afghanistan, domin farfado da kasar bisa iyakacin kokari. Ya ce Sin na fatan zurfafa hadin gwiwa tsakanin ta da Afghanistan a duk fannoni, domin cimma moriyar juna, musamman ma a fannonin samun ci gaba da tabbatar da tsaro.

A nasa bangare, Mr. Rabbani ya bayyana cewa, kasar Afghanistan ta jinjinawa kasar Sin tare da yaba irin muhimmiyar rawar da take takawa a fannin wanzar da zaman lafiya da sulhu da kuma ci gaba a Afghanistan. Daga nan sai ya yi fatan kasashen biyu za su kara kokari a fannin cimma moriyar juna. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China