in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a gaggauta fara shawarwari sulhu domin warware matsalar Syria, in ji ministan harkokin wajen Sin
2015-12-24 20:28:10 cri

A yau Alhamis ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Syria, kana mataimakin firaministan kasar Walid al-Moallem wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin a halin yanzu.

A yayin ganawarsu, Wang Yi ya bayyana cewa, manyan ayyuka biyu da ke gabansu wajen aiwatar da kuduri mai lamba 2254 da kwamitin sulhu ya zartas da shi su ne, yin shawarwarin neman sulhu da kuma tsagaita bude wuta a kasar Syria.

Don haka yana fatan gwamnatin kasar Syria za ta fara tattaunawa da kungiyoyin adawa bisa taimakon MDD, ta yadda za a warware matsalolin da abin ya shafa domin ci gaba da shawarwarin yadda ya kamata. A sa'i daya kuma, ya kamata a ciyar da aikin tsagaita bude wuta a yankuna da dama gaba, har ma da duk fadin kasar. Haka kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, sabo da yadda kasar Sin ke nuna damuwa kan halin da al'ummomin kasar Syria ke ciki, Sin za ta kara samar da taimakon kudi Yuan miliyan 40 ga Syria domin samar da taimakon jin kai, inda za a yi amfani da kudaden wajen gina kayayyakin more rayuwa a kasar.

A nasa tsokaci, Walid al-Moallem ya ce, gwamnatin kasar Syria tana shirin tattaunawa da kungiyoyin adawar kasar, za kuma ta aike da wata tawaga zuwa birnin Geneva na kasar Switzerland domin halartar shawarwarin, da zarar kungiyoyin adawa su gabatar mata da jerin sunayen mambobinsu. Kaza kila, ya ce, kasarsa na nuna godiya matuka ga taimakon jin kai da kasar Sin ta samar mata, kuma tana fatan gamayyar kasa da kasa za su taimaka wajen sake gina kasar ta Syria. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China