Kaza lika, a karkashin wannan kuduri, mahukuntan kasar Syria, da hukumomin jin kai na MDD suna da ikon ratsa wurare hudu na kan iyakar kasar ta Syria da kasashen Turkiya, da Iraki, da Jordan, bayan sun sanar da mahukuntan kasar Syria. Domin samar da kayayyakin jin kai zuwa wurare daban daban na kasar Syria.
Mataimakin wakilin Sin dake MDD Wang Min, ya gabatar da jawabi bayan zartas da kudurin, ya na mai cewa Sin ta yi maraba da kwamitin don gane da zartas da kudurin mai lamba 2258. Ya ce Sin na goyon bayan hukumomin jin kai na MDD, wajen gudanar da ayyukan jin kai bisa tushen girmama ikon mulkin kasar Syria, domin daidaita kasa da kasa da su ba da gudummawa. Sin ta yi kira ga bangarori daban daban da wannan batu ya shafa, da su sauke nauyin dake kan su na aiwatar da sabon kuduri, da ma sauran kudurorin dake da alaka da shi, tare da tabbatar da samar da gudummawar jin kai, da sassauta mawuyacin halin da jama'ar kasar Syria ke ciki.
Wang Min ya kara da cewa, hanyar siyasa ita ce hanya daya kacal ta warware batun kasar Syria, kana ita ce tushen kyautata halin jin kai na al'ummar kasar, da ma magance matsalar 'yan gudun hijirar Syrian. (Zainab)