Konashenkov ya bayyana wa 'yan jarida hakan a jiya Laraba, yana mai cewa jirgin saman yakin na Rasha ya lalata sansanonin ajiye man fetur biyu, da na'urorin hakar man fetur uku na 'yan ta'adda a yankin Deir ez-Zor dake kasar Syria, a farmakin da ya kai ranar 22 ga watan nan. Ya ce Jirgin saman yakin na Rasha zai ci gaba da kai hari ga wuraren da ake gudanar da ayyukan hakar man fetur na 'yan ta'adda dake kasar Syria.
Konashenkov ya kara da cewa, jirgin saman yakin na Rasha ya kuma lalata wani sansanin horar da 'yan ta'adda dake jihar Idleb ta kasar Syria a dai ranar ta 22 ga wata.
Ban da wannan kuma, Konashenkov ya ce, jirgin yakin ya yi sawu fiye da 300 a cikin kwanaki biyar, inda ya kai farmaki a wurare 1093 dake Aleppo, da Idleb, da Deir ez-Zor, da Hama, da Homs da dai sauransu, duka a kasar ta Syria. (Zainab)