Mr. Wang ya ce, a farkon wannan shekarar, shugaba Xi Jinping ya kai ziyara a kasashen Saudiya, da Masar, da kuma Iran ne, domin kaddamar da muhimmin aikin diplomasiyya na farko a bana. Wadannan kasashe uku suna da babban tasiri a yankin Gabas ta Tsakiya. Akwai dankon zumunci tsakaninsu da Sin, haka kuma suna gudanar da hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban daban. Sau da yawa shugabannin kasashen uku sun gayyaci shugaba Xi domin kai ziyara a kasashensu. A wannan karo, shugaba Xi ya karbi goron gayyatar tare da mai da ziyara a matsayin ziyara ta farko da ya kai ketare a bana. Wannan ya bayyana muhimmancin da Sin ta dora kan bunkasa dangantaka tsakaninta da wadannan kasashen uku, har ma da yankin Gabas ta Tsakiya.
A yayin ziyararsa, shugaba Xi ya kai ziyara a birane hudu cikin kwanaki biyar, inda ya halarci ayyuka sama da 40, tare da yin shawarwari da shugabannin kasashen uku da shugabannin kungiyoyin shiyya shiyya guda uku. Baki daya, an rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa 52 a yayin wannan ziyara. Ziyarar shugaba Xi a yankin Gabas ta Tsakiya a wannan karo, ta sami babbar nasara, inda aka cimma burin sada dankon zumunci, da yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, da sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a wannan yanki, da kuma sa kaimi ga samun ci gaba da zaman lafiya a kasa da kasa baki daya.(Fatima)