in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron tattaunawa tsakanin kafofin watsa labaru na kasashen Sin da Iran
2016-01-23 13:32:09 cri
A ranar 22 ga wata, wato gabannin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Iran, an shirya taron tattaunawa tsakanin kafofin watsa labaru na kasashen biyu, inda daraktan ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Jiang Jianguo ya ba da jawabi.

A cikin jawabinsa, mista Jiang ya gabatar da shawarwari a fannoni guda uku game da yadda za a samu nasarar watsa labaru kan ziyarar shugaba Xi a Iran.

Da farko, yana fatan kafofin watsa labaru na kasashen biyu su yi kokari tare, don watsa labaru kan wannan ziyara kamar yadda ya kamata. Saboda wannan ita ce ziyara ta farko ta shugaba Xi a kasar Iran bayan ya dauki karagar mulkin shugaban kasar Sin, da kuma take jawo hankulan kasashen duniya, yankin Gabas ta Tsakiya da ma kafofin watsa labaru na duniya baki daya. A yayin ziyarar, shugaba Xi zai gabatar da wani shiri game da warware muhimman matsalolin da ake fuskanta a shiyyar, kana zai mayar da hankali kan raya "Zirin tattalin arziki na hanyar siliki, da hanyar siliki kan teku ta karni na 21", wato "Ziri Daya da Hanya Daya" a takaice a tsakanin kasashen Sin da Iran, tare kuma da gabatar da jerin muhimman matakai.

Na biyu, yana fatan kafofin watsa labaru na kasashen Sin da Iran za su taka rawar kara zumunta tsakanin kasashen biyu da yin mu'amalar al'adu tsakaninsu.

Na uku, yana fatan kafofin watsa labaru na kasashen biyu za su yi kokari don ciyar da ayyukan hadin kai da cudanya a tsakaninsu gaba.

A nasa bangare, wani jami'in ma'aikatar jagoranci kan al'adun musuluncin kasar Iran ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, kafofin watsa labaru na iya kara ba da gudummowarsu ta hanyar yin cudanya domin wayewar kan al'ummomi daban daban, da kuma kawar da matsalolin da suka shafi rashin daidaito da adalci a yayin da ake watsa labaru. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China