A jiya Alhamis ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a hedkwatar kungiyar hada kan kasashen Larabawa dake Alkahira, fadar mulkin kasar Masar, inda ya yi bayani kan manufofin da kasarsa ke aiwatarwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan a taimaka wajen cimma burin shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, kuma tana fatan za a kara mai da hankali kan moriyar al'ummomin kasashen da ke shiyyar yayin da ake tsara tsarin dake shafar kasashen.(Jamila)