in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan bude wani sabon babi na yin hadin gwiwa da cimma moriyar juna tsakanin Sin da Iran
2015-07-15 18:47:25 cri

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya bayyana cewa za a bude wani sabon babi na hadin gwiwa, da cimma moriyar juna tsakanin Sin da Iran, karkashin shirin aiwatar da yarjejeniyar daidaita batun nukiliyar kasar ta Iran.

Mr. Wang ya bayyana hakan ne jiya Talata, yana mai cewa Sin za ta taka muhimmiyar rawa, wajen kyautata tsarin tashar sarrafa sinadarin nukiliya a Arak dake kasar ta Iran, bayan daddale yarjejeniyar warware batun nukiliyar ta Iran tsakanin sassan masu ruwa da tsaki.

Mr. Wang ya kara da cewa, kyautata tashar ta Arak, wani muhimmin kashi ne cikin shawarwarin da aka kammala game da warware matsalar nukiliyar ta Iran.

Bayan kokari daga bangarorin daban daban, yanzu haka an riga an tabbatar da cewa za a kafa wani hadadden rukunin zartaswa na bangarori shida, a karkashin jagorancin kasashen Sin da Amurka. Duba da cewa kasar Sin ce ta fitar da wannan ra'ayi na kyautata tashar Arak, ya sa za ta rungumi aikin tare da Iran, duka dai da nufin sa kaimi ga gudanar wannan aiki cikin nasara.

Wannan dai ya zamo daya daga cikin ayyuka na musamman da Sin ta yi, a fannin warware matsalar nukiliyar kasar ta Iran. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China