in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da cimma daidaito a tsakanin kasashe 6 da Iran kan aiwatar da yarjejeniya a mataki na farko
2014-01-13 20:19:15 cri
Kasar Sin ta yi maraba da cimma daidaito a tsakanin kasashe 6 da kasar Iran dangane da yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a mataki na farko. Ta kuma yaba wa kokarin da bangarorin da abin ya shafa suke bayarwa ta fuskar diplomasiyya, a cewar madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a ranar 13 ga wata.

Madam Hua ta bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing. Ta kara da cewa, kasar Sin na fatan bangarorin daban daban za su yi kokari tare domin ganin an aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata. Sa'an nan kuma, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan yin shawarwari cikin adalci kan abubuwan da suka biyo baya, a kokarin cimma yarjejeniyar daga dukkan fannoni cikin sauri.

Madam Hua ta jaddada cewa, kasar Sin na son ci gaba da tuntubar bangarorin daban daban wajen yin shawarwari yadda ya kamata. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China