Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Masar Abdul Fatah Al-Sisi, sun halarci bikin murnar cika shekaru 60 da kulla dangantaka tsakanin kasashen biyu, kuma an gudanar da bikin nuna al'adu na wannan shekarar na kasashen biyu a ranar 21 ga wannan wata a wajen ibada na Luxor da ke kasar ta Masar.
Bayan da shugabannin kasashen biyu suka shiga wurin ibada, sun tofa albarkacin bakinsu game da daddaden tarihi da al'adun kasashen biyu, kuma sun waiwayi mu'amalar kasashen biyu. Shugaban Xi ya yi nuni da cewa, kasashen Sin da Masar suna da dadadden tarihi, ya zama wajibi kasashen biyu su inganta mu'amalar al'adu da zurfafa sada zumunta a tsakanin jama'a, don karfafa bangarorin biyu domin su samu bunkasuwa da wadata. Shugaban Al-Sisi na Masar ya bayyana halartar bikin da shugaban Xi yayi da cewa, kasar Sin na nuna goyon baya ga Masar. Sannan ya bukaci kasashen biyu su inganta musayar al'adu, don ci gaba da zama aminan juna.(Bako)