Cikin sanarwar, kwamitin ya kuma bayyana cewa, muddin za a aiwatar da tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar da aka cimma, hakika za a kyautata yanayin tsaro a kasar Mali.
Haka kuma, ya ce, ya kamata gwamnati da kuma kungiyoyin dakarun kasar Mali su yin kokarin da ake na shimfida zaman lafiya a kasar ta Mali, ana kuma kira a gare su da su dauki matakan da suka dace na ganin an aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, haka kuma, ana yin kira a gare su da su hanzarta hadin gwiwa bisa dukkan fannoni wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar.
Kwamitin ya kuma bukaci gwamnatin kasar Mali da kungiyoyin dakarun kasar da su fara yin sintiri domin tabbatar da tsaro a arewacin kasar da kuma kawar da kwance damarar makamai dake hannun dakarun da dai sauransu kamar yadda aka tsara a cikin yarjejeniyar.
Kaza lika, kwamitin sulhu na MDD ya yi kira ga sabon wakilin magatakardan MDD kan batun kasar Mali da ya dukufa kan aikin shiga tsakani, domin nuna goyon baya da kuma sa ido kan bangarorin da abin ya shafa wajen gudanar da yarjejeniyar zaman lafiya yadda ya kamata. (Maryam)