in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mali: Za'a tsawaita dokar ta-baci har zuwa watanni uku
2015-12-30 10:29:38 cri
Dokar ta baci dake aiki a yanzu haka a kasar Mali, za a tsawaita ta da watanni uku har zuwa 31 ga watan Maris, a cewar wani shirin doka da aka cimma a ranar Litinin a yayin wani zaman taron ministoci na musamman. Dokar ta bacin dake aiki a yanzu an aiwatar da ita ta hanyar wani kuduri na ranar 21 ga watan Disamba, a kusantowar bukukuwan karshen shekara da kuma bukin mauludi domin karrama ranar aifuwar manzon Allah Annabi Mohammed (SAW), bisa dalilai na babbar barazana kan tsaron jama'a da dukiyoyinsu. Da ya kamata kuma ta kawo karshe a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2015 a tsakiyar dare. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China