in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mambobin tsofuwar kungiyar 'yan tawaye ta CMA shida a kasar Mali
2015-12-27 14:26:49 cri
A kalla mambobi shida na kawancen kungiyoyin tsoffin 'yan tawaye na Azawad (CMA) aka kashe a ranar Jumma'a a yayin da wasu mayakan masu kishin islama suka kai wani hari a sansaninsu, dake kusa da iyaka da kasar Aljeriya. Sansanin CMA, da wata kungiyar 'yan ta'adda dauke da manyan makamai da suka zo kuma cikin motoci kirar pick-up da aka kai ma hari na yankin Talahandak, kusa da iyaka da Aljeriya, wani yankin kai da kawo na masu sumogal kana kuma wata mahada dake bada damar zuwa Nijar da Aljeriya.

Motocin goma sha biyar ne suka hade cikin mutane da aka yi amfani dasu a matsayin garkuwa, in ji Ambery Ag Rhissa, mamba na CMA da rediyo Tamani ya rawaito maganarsa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China