Wannan rance zai taimaka a cewar wata sanarwa, wajen kyautata mulki na gari, da kafa damammakin tattalin arziki da karfafa karfin jurewa fargaba da wasu matsaloli.
Muhimman kalubalolin rage talauci da kuma bunkasa wani alheri ga kowa a kasar Mali sun kasance na rashin tsarin mulki na gari, rashin karfin samar da albarkatun noma daga wajen manoma da masu kiwo da kuma rashin inshorar hadari, in ji Paul Noumba Um, darektan ayyukan Bankin duniya dake Mali, da aka ruwaito cikin sanarwar.
Sabon tsarin na da manufar maida hankali kan wadannan matsaloli ba tare da wani jinkiri ba da kuma samar da hanyoyin warware yadda ya kamata daga bangaren gwamnatin da kuma zuwa kananan hukumomi, in ji mista Paul Noumba.
A cewar bankin duniya, kawar da matsalar tsaro ita ce babban matakin cigaban maradun rage talauci da kawo sauye sauyen tattalin arziki mai dorewa a kasar Mali. (Mali)