Kwamishina mai lura da al'amurran tsaro da zaman lafiya na kungiyar AU Smail Chergui, ya ce matsalar karuwar ayyukan ta'addanci da munanan laifuka ne suka tilasta kungiyar ta AU daukar wannan mataki na tura Karin jami'an, domin samar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.
Kungiyar Afrika mai samar da tallafi a kasar Mali wato AFISMA, ta tura jami'an aikin wanzar da zaman lafiya a farkon shekarar 2013, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewacin Mali, bayan bullar mayakan kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a kasar.
A watan Yuli, tawagar kungiyar ta Afrika tare da hadin gwiwar hukumar samar da zaman lafiya ta MDD a kasar Mali wato MINUSMA, ta jagoranci yarjejeniyar zaman lafiya da tattaunawar sulhu tsakanin kungiyoyin 'yan tawayen kasar Mali. To sai dai kungiyoyi 'yan ta'adda na kasar sun ci gaba da kaddamar da hare hare kan jami'an na MINUSMA , kuma matakin, ya yi sanadiyyar gurgunta shirin zaman lafiya a kasar.(Ahmad Inuwa)