A kasar Mali, duk da dokar ta bacin da aka sanya a ranar Litinin bisa tsawon kwanaki goma, bakukuwan karshen shekara da mauludi wato bikin salar da musulmi suke yi domin girmama ranar haifuwar Manzon Allah (SAW) za a gudana da su, in ji ministan tsaron kasar Mali, kanal manjo Salif Traore, a yayin wani taron menama labarai a ranar Laraba a birnin Bamako.
Dokar ta baci ba a sanya ta ba domin hana ganin ayarin motoci, kide kide ko gudanar da bukukuwa a wannan karshen shekara ba, in ji mista Salif Traore, barazanar da kasar Mali take fuskanta da ma a wasu manyan birane na shiyyoyi na bukatar a rika yin taka tsantsan da daukar matakan rigakafi. (Maman Ada)