Jami'an kwastan a kasar Mali sun kama kilogram dari biyar na hodar ibilis wanda aka kiyasta darajarsa zuwa Sefa miliyan 659. Ma'aikatan kwastan din sun yi wannan kamu a Nioro de Sahel dake arewa maso yammacin yankin Kayes. Hodar ibilis an boye ta a cikin wata motar da ta fito daga kasar Marocco da kuma zata wuce kasar Aljeriya tare da ratsa Mali da Mauritaniya, da direbanta wani dan kasar Marocco ne.
Bayan wannan kamu na hodar ibilis, kwastan kasar Mali sun gano wata sabuwar hanyar da masu sumogal din miyagun kwayoyin suke amfani da ita domin isa zuwa kasashen Turai. (Maman Ada)