A jawabinsa mataimakin ministan kudi na Sin, Zhu Guangyao ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen BRICS su kara kokarin tattara kudaden tafiyar da bankin. Ya ce, bankin bunkasuwa na BRICS zai taimaka ga tsarin hada hadar kudi na duniya, haka kuma zai kasance gwaji wajen yin kwaskwarima da kyautata tsarin hada hadar kudi na duniya.
Shugaban sashen kula da harkokin kasa da kasa a ma'aikatar kasuwanci ta Sin, Zhang Shaogang ya bayyana ra'ayinsa kan yadda za a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS biyar a fannin cinikayya. Ya ce, a shekarar 2014, jimillar kudin cinikayya tsakanin wadannan kasashe biyar ta kai dala biliyan 350, wadda ta kai kashi 10 cikin dari kawai bisa jimillar kudin cinikayya da kasashen BRICS suka yi da sauran kasashen duniya, don haka akwai babbar damar yin hadin gwiwa tsakaninsu. A nan gaba, kamata ya yi a tabbatar da tsarin yin hadin gwiwa tsakaninsu a fannin tattalin arizki yadda ya kamata, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin yin kasuwanci ta hanyar yanar gizo, da ikon mallakar fasaha da dai sauransu.
A nasa bangare, jakadan Brazil da ke nan kasar Sin, Roberto Jaguaribe ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen BRICS su kara inganta manufofinsu na yin hadin gwiwa. Ya ce, kasashen BRICS suna samun moriyar juna, don haka kamata ya yi su kara cimma daidaito kan manufofin juna, ta yadda za su ci gajiyar juna a fannin tattalin arziki yadda ya kamata.(Fatima)