in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fidda sanarwar bayan taron masu ruwa da tsaki game da harkokin watsa labarai na kungiyar BRICS
2015-12-01 19:22:42 cri
A talatar nan ne aka kammala taron masu ruwa da tsaki game da harkokin watsa labarai, na kungiyar kasashen masu tasowa da ke gaba-gaba a bunkasar tattalin arziki wato BRICS.

Mahalarta taron na yini guda daga kungiyoyi da cibiyoyi 25 na kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, sun fidda wata sanarwa hadin gwiwa dake tabbatar da amincewar su, da manufar zurfafa hadin kai da juna. Sanarwar ta ce mahalartan sa na fatan wanzar da hadin gwiwa tsakanin kasashe 5 mambobin kungiyar, musamman a fannin bunkasa tattalin arziki, da zamantakewa, da siyasa cikin adalci da daidaito, baya ga samarwa duniya sahihan bayanai masu inganci.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ne ya shirya taron, tare da hadin gwiwar cibiyoyin yada labarai na kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya da kuma Afirka ta kudu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China