in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi taron kafofin watsa labarai na kasashen BRICS karo na farko a Beijing
2015-11-28 15:51:15 cri
Za a yi taron kafofin watsa labarai na kasashen BRICS karo na farko a birnin Beijing a ran 1 ga watan Disamba mai zuwa, inda walikan kafofin watsa labarai guda 25 na kasashen BRICS za su halarta.

Taron da ya zabi "yin sabuntawa domin neman ci gaba da kuma yin hadin gwiwa bisa fahimtar juna" a matsayin babban taken shi, ya kuma kafa reshen dandalin tattaunawa guda uku da ake kira "amfanin kafofin watsa labarai wajen inganta dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen BRICS", "karfafa mu'amala da hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labarai na kasashen BRICS" da kuma "yadda za a daidaita bunkasuwa da hadin gwiwar kafofin watsa labarai na gargajiya da na zamani".

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, kamfanin dillancin labaran kasar ta Brazil, kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Russian Today, jaridar Hindu ta kasar Indiya da kuma kamfanin dillancin labarai na Independence na kasar Afirka ta Kudu suka kira wannan taro cikin hadin gwiwa, kana kamfanin dillancin labarai na Xinhua za ta gudanar da taron karo na farko. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China