in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta Kudu ya yaba wa hadin gwiwar kungiyar kasashen BRICS
2015-08-07 10:50:02 cri
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya furta a jiya Alhamis 6 ga wata cewa, yayin da yawan cinikin da ke tsakanin kungiyar kasashen BRICS ya kara karuwa, kasarsa tana cin gajiya daga cikin irin hadin gwiwa na kungiyar, ciki har da bankin raya kungiyar BRICS da aka kafa.

Shugaba Zuma ya fadi hakan ne, yayin da yake zantawa da 'yan majalisun dokokin kasar. Wasu 'yan majalisun kasar suna fata shugaba Zuma zai bayyana halin da ake ciki game da hadin gwiwa da kuma saka jari tsakanin kasar da sauran abokan hulda na kungiyar kasashen BRICS da ma ragowar kasashe masu tasowa. Shugaban Zuma ya ce, tun daga shekarar 2009 zuwa yanzu, yawan cinikin da ke tsakanin mambobin kasashen BRICS ya karu da kashi 70 cikin 100. A shekarar 2014, kungiyar BRICS ta jawo jarin kai tsaye da yawansa ya kai kashi 20.5 cikin 100 a duniya, kuma wannan adadin ya karu sosai idan aka kwatanta shi da kashi 16.9 cikin 100 da aka samu a shekarar 2009.

Kazalika, shugaba Zuma ya bayyana yanayin da ake ciki a gun taron kolin kungiyar kasashen BRICS da aka yi a birnin Ufa da ke kasar Rasha. Ya yi nuni da cewa, muhimmin sakamakon da aka samu a yayin taron koli shi ne, an bude bankin raya kasashen BRICS, abun da ya samar da wani sabon dandali ga gamayyar kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki, kuma ya yi farin cikin ganin cewa, nagartattun jami'an bankin kasarsa guda 2 sun zama darektocin gudanar da bankin raya kasashen BRICS.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China