Ministan kudi na kasar Sin Lou Jiwei, da magajin garin birnin Shanghai Yang Xiong da shugaban bankin na NDB K.V. Kamath daga kasar Indiya sun halarci bikin.
A jawabinsa yayin wani taron karawa juna sani bayan kaddamar da bankin Mr Lou ya ce, bankin zai taimakawa tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa ta hanyar da ta dace tare da bullo da matakan tafiyar da harkokin mulki.
A ranar 7 ga watan Yulin wannan shekara ce, kasashen na BRICS da suka hada da Brazil, Rasha, Indiya, Sin da kuma Afirka ta kudu suka kaddamar da bankin raya kasa na biliyoyin daloli yayin taron kolin kungiyar karo na 7 da ya gudana a birnin Ufa na kasar Rasha da nufin samar da ababen more rayuwa, musamman a kasashe mambobin kungiyar. (Ibrahim)