in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sashen kasuwanci na Afrika ta Kudu ya nemi a baiwa mambobin kasahen BRICS takardun izinin shiga kasashe kyauta
2015-08-19 10:47:34 cri

Sashen al'amurran kasuwanci na Afrika ta Kudu ya yi na'am da matakin da kasar Rasha ta dauka na samar da takardun izinin shiga kasar kyauta ga masu yawon bude ido wadanda suka fito daga kasashen China da India da Brazil da kuma Afrika ta Kudu wato BRICS a takaice.

Shugaban kwamitin kasuwanci na kungiyar ta BRICS Brian Molefe, ya shedawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewar, muddin aka bude kofofin huldar kasuwanci ko kuma aka baiwa al'ummomin wadannan kasashe takardun izinin shiga kasar na shekara da shekaru kyauta, to babu tantama hakan zai taimaka matuka wajen bunkasar huldar kasuwanci tsakanin kasashen.

A cewar Molefe, muddin aka bude kofar kasuwancin, ana sa ran cikin ko wane wata, za'a samar da guraben aiki da ba su gaza miliyan 3 ba ga 'yan wadannan kasashe.

Wasu kungiyoyin 'yan kasuwa a Afrika ta Kudu suna ta fafutukar ganin an soke takardun izinin zirga-zirga tsakanin mambobi kasashen na BRICS domin a cewar su hakan zai saukaka harkokin zirga-zirga da kuma cinikayya tsakanin kasashen.

Kwararru a fannin kasuwanci sun ce sanya tsauraran dokoki da Afrika ta Kudu ta yi wajen neman takardun izinin shiga kasar shi ne babban abin da ke haifar da koma baya a sha'anin kasuwanci tsakanin mambobin na BRICS. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China