in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Iraki za ta warware rikicin da ke tsakanin ta da Turkiya ta hanyar siyasa, in ji jaafari
2015-12-14 09:50:03 cri
Ministan harkokin wajen kasar Iraki Ibrahim Jaafari ya bayyana cewa, kasarsa za ta yi amfani da matakan siyasa wajen warware takaddamar da ta kunno kai tsakaninta da kasar Turkiya, ta yadda ba za a keta 'yancin kasar ta Iraki ba

Minista Jaafari ya bayyana hakan ne kwanaki uku bayan da shugaba Recep Tayyib Erdogan ya ce sun jibge sojoji a yankin arewacin kasar ta Iraki ne domin samar da horo, don haka ba su janye su ba.

Don haka ya ce, Iraki na maraba da duk wani taimakon da zai hana duk wasu dakaru shiga ko mamaye yankunan kasar ba tare da izni ba.

Ministan Jaafari ya ce, Iraki ba za ta lamunci kowa ce kasa ta gina sansanoninta na soja a cikin yankunan Iraki ba, yin hakan a cewarsa,tamkar bude kofa ce ga karin kasashe su baje kolin su a kasar.

Yanzu dai kasar Irakin za ta karkata ga yin amfani da hanyoyi na diflomasiya wajen kawo karshen kutsen da kasar Turkiya ta yi a kasar, don ganin lamarin bai rikide zuwa wani sabon rikici ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China