Birnin Ramadi dai shi ne babban birnin jihar al-Anbar, jiha mafi girma a kasar ta Iraki. Tun kuma cikin watan Mayu na wannan shekara ne kungiyar IS ta mamaye shi, inda mayakan ta suka maida shi muhimmin sansanin su a yammacin kasar.
Rundunar sojin kasar ta fayyace cewa, tun da fari ta kwace wani matsugunin kungiyar dake cibiyar birnin Ramadin, kafin daga bisani ta mamaye babban ginin gwamnatin jihar dake wurin.
Birnin Ramadi na da muhimmin matsayi, kuma kwace shi daga hannun mayakan na IS zai taimakawa sojojin gwamnatin mamaye biranen Fallujah, da Mosul daga ikon kungiyar ta IS.
Rahotanni sun nuna cewa, fadin yankunan kasar da kungiyar IS ke mamaye da su na ci gaba da raguwa. Kaza lika jaridar harkokin tsaro ta Jane's Defence Weekly ta kasar Birtaniya, ta fidda wani rahoto dake cewa, a shekarar 2015 din nan, fadin yankunan da kungiyar ta mallaka a kan iyakar kasashen Iraki da Sham, ya ragu da kashi 14 cikin dari.(Lami)