in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai harin kunar bakin wake a wani wuri dake dab da sansanin sojojin kasar Amurka dake Iraki
2016-01-04 10:43:16 cri

Rundunar sojan tsaro ta kasar Iraki, ta ce a kwanan baya kungiyar IS ta kai harin kunar bakin wake a wani wuri dake dab da wani sansanin sojojin kasar Amurka dake birnin Tikriti, fadar mulkin jihar Salahudin ta kasar Iraki, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin tsaron kasar a kalla 15, a yayin da mutane 22 suka ji raunuka.

An ba da labari cewa, dakaru sun yi shirin kai harin ne kan 'yan sandan jihar Ninewa, wadanda ke samun horo a cikin sansanin. Dakaru 2 ne dai suka tada boma-bomai a gaban kofar sansanin, saura ukun kuma sun tada boma-boman dake jikin su bayan sun kutsa kai cikin sansanin.

Tuni dai kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai wannan hari a kan shafin ta na yanar gizo.

A ranar 28 ga watan Disambar da ya gabata ne, sojojin gwamnatin Iraki suka sanar da cewa, sun kwace birnin Ramadi daga hannun kungiyar IS, kuma nan gaba kadan za su yi yunkurin kwato jihar Ninewa. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China