Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya jagoranci a ranar Litinin a birnin Alger wani taron ministoci wanda a karshe ya amince da shirin kawo gyaran fuska ga kundin tsarin mulki.
Matakin farko na wannan shirin kawo gyara, shugaban kasa ya amince da shi a karshen watan Disamba kana darektan fadar shugaban kasa Ahmed Ouyahia ya gabatar a ranar Talata, na kunshe da wasu muhimman matakai, kamar amincewa da harshen Tamazight a matsayin harshen aiki da kuma tsai da zuwa biyu adadin wa'adin shugaban kasa na shekaru biyar.
Yanzu matakin karshe na wannan muhimmin kundin doka ya samu amincewa, kuma za a gabatar da shi a gaban majalisun kasar biyu, da kwamitin kasa da kuma yiwuwar isar da shi ga zaben raba gardama. (Maman Ada)