Manufar gwamnatin ita ce takaita kashe kashen kudin gwamnati. Amma wannan manufa ba wai tana nufin tsuke bakin aljihu ba, in ji mista Sellal a yayin wata ziyarar aiki da ya kai a Wilaya da ke karkarar birnin Alger, tare da nuna cewa faduwar farashin man fetur wata dama ce domin canja siyasar tattalin arzikin kasar bisa manufar fita da yin dogaro da man fetur da kuma kafa wasu hanyoyin samun arziki da ayyukan yi.
Bayan jerin faduwar farashin danyen mai, wanda kudaden fitar da man fetur ke wakiltar kashi 95 cikin 100 na kudin shigar da kasar take samu, gwamnatin Aljeriya ta sanar da daukar matakai, wanda suka hada da soke sabbin ma'aikatun dake lakume kudi a cikin harkokin gwamnati da kuma dakatar da wasu ayyukan gine ginen ababen more rayuwa. (Maman Ada)